Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin shekara 20

Wata kotu a kasar Kwaddibuwa ta yanke wa matar tsohon shugaban kasar, Simone Gbagbo hukuncin shekara 20 a gidan kaso saboda irin rawar da ta taka a rikicin bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2010. A shekarar 2011 ne dai aka kama Simone Gbagbo tare da mai gidanta, Laurent Gbagbo bisa dalilan yin zagon kasa […]

Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin shekara 20
Kotu ta yanke wa Simone Gbagbo hukuncin shekara 20

Wata kotu a kasar Kwaddibuwa ta yanke wa matar tsohon shugaban kasar, Simone Gbagbo hukuncin shekara 20 a gidan kaso saboda irin rawar da ta taka a rikicin bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2010.

A shekarar 2011 ne dai aka kama Simone Gbagbo tare da mai gidanta, Laurent Gbagbo bisa dalilan yin zagon kasa ga yanayin tsaro da kuma karfafa wa ‘yan bangar siyasa gwiwa a lokacin rikicin zaben.
Shi dai mista Gbagbo yaki amince wa da kayen da yasha daga abokin hamayyarsa, Mista Alassane Ouattara wanda duniya ta bayyana da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar na shekarar 2010. Kimanin mutane dubu uku ne suka rasa rayukansu a lokacin rikicin.
A lokacin zaman kotun, sai da ’yan sanda suka shiga tsakanin magoya bayan Gbagbo da masu adawa da shi a daidai lokacin da wata hatsaniya ta barke a harabar kotun. Har ila yau, ma’aikatar shari’ar kasar ta dage sai ta yi wa Misis Simone Gbagbo shari’a a gida madadin bukatar da kotun hakunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, wato ICC na yi ma ta shari’a a birnin Hague. Kuma ita da fiye da mutum 80 masu goyon bayan Gbagbo an tuhume su ne da raina hukuma. Hakazalika, ana zargin duka bangarorin biyu da hannu a rikicin da ya biyo bayan zaben
A yanzu haka, Laurent Gbagbo yana fuskantar tuhuma daga kotun ICC bisa dalilan keta haddin dan Adam. An kama shi wata biyar bayan zaben sakamakon harin da dakarun Majalisar dinkin Duniya da sojojin kasar Faransa suka kai a wani gidan karkashin kasa da yake boye.