Kotu ta yanke wa tsohon Firaministan Isra’ila daurin shekara 6
Wata kotun birnin Tel Abib a kasar Isra’ila ta yanke wa tsohon Firaministan kasar Ehud Olmert daurin shekara shida bayan samunsa da laifin kabar cin-hanci a wata badakalar lokacin da yake magajin garin Jerusalam.Sai dai Mista Olmert ya musanta laifin da ake tuhumarsa. Wannan ya sa lauyoyinsa suka bukaci kotun da ta jinkirta hukuncin har […]

Wata kotun birnin Tel Abib a kasar Isra’ila ta yanke wa tsohon Firaministan kasar Ehud Olmert daurin shekara shida bayan samunsa da laifin kabar cin-hanci a wata badakalar lokacin da yake magajin garin Jerusalam.
Sai dai Mista Olmert ya musanta laifin da ake tuhumarsa. Wannan ya sa lauyoyinsa suka bukaci kotun da ta jinkirta hukuncin har sai bayan hukuncin kotun kolin kasar. Idan dai bai samu nasara ba, zai zama tsohon shugaba na farko a kasar da zai yi zaman wakafi.
Alkalin kotun Dabid Rozen ya same shi da laifin karbar cin-hanci da ya kai Dala dubu 161 wanda ya zo daidai da Naira miliyan 26 da dubu 565. Mai shari’ar ya kuma ce cin-hanci da karbar rashawa abubuwa biyu ne da ke ruguza cibiyoyin gwamnati. A karkashin dokar kasar dai, ba zai iya rike wani mukamin gwamnati ba har sai bayan ya shekara bakwai da kammala zaman jarun.
Mista Olmert dai ya shugabanci kasar Isra’ila ne daga shekarar 2006, kafin ya sauka a 2009 saboda dalilan zargin cin-hanci da rashawa da ake masa.