Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Masar daurin shekara 3
A shekaranjiya Larabar ne wata kotun kasar Masar ta yanke wa tsohon shugaba Hosni Mubarak hukuncin daurin shekara uku a gidan yari bayan samunsa da laifin almabazaranci da dukiyar al’umma.’Ya’yansa biyu, Alaa da Gamal su kuma kotun ta yanke musu hukuncin shekara hudu kowanensu. Mai gabatar da kara dai ya tuhumi Mubarak ne da sace […]
A shekaranjiya Larabar ne wata kotun kasar Masar ta yanke wa tsohon shugaba Hosni Mubarak hukuncin daurin shekara uku a gidan yari bayan samunsa da laifin almabazaranci da dukiyar al’umma.
’Ya’yansa biyu, Alaa da Gamal su kuma kotun ta yanke musu hukuncin shekara hudu kowanensu. Mai gabatar da kara dai ya tuhumi Mubarak ne da sace Dala miliyan 17 da dubu dari 6 (wanda ya yi daidai da Naira biliyan 29 da miliyan hudu) wadanda aka kebe don aikin kwaskwarimar fadar shugaban kasar.
Har ila yau, ana tuhumar tsohon shugaban da amfani da iko ba bisa ka’ida ba, da kuma hadin baki don kisan masu zanga-zanga a lokacin da ake boren da ya tilasta masa sauka daga mulki a shekarar 2011. Kafin saukarsa dai, ya kwashe shekara kusan 30 ya na mulkin kasar.