Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Turkiyya daurin rai-da-rai
A shekaranjiya Laraba ne wata kotun da ke birnin Ankara ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Turkiyya, Kenan Ebren da kuma tsohon Kwamandan Sojin Saman kasar Tahsin Sahinkaya hukuncin daurin rai-da-rai saboda rawar da suka taka a juyin mulkin watan Satumban shekarar 1980.Mista Ebren mai shekara 96 da kuma Mista Sahinkaya wanda yake da shekara […]

A shekaranjiya Laraba ne wata kotun da ke birnin Ankara ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Turkiyya, Kenan Ebren da kuma tsohon Kwamandan Sojin Saman kasar Tahsin Sahinkaya hukuncin daurin rai-da-rai saboda rawar da suka taka a juyin mulkin watan Satumban shekarar 1980.
Mista Ebren mai shekara 96 da kuma Mista Sahinkaya wanda yake da shekara 89, an tuhume su ne da samar da yanayin da ya haifar da juyin mulki da kuma jagorantarsa.
Ebren ya zama zabebban shugaban kasar ne bayan ya shugabance ta a matsayin shugaban mulkin soja. Kuma bai taba bayyana nadamarsa da juyin mulki ba, wanda ya ce ya jagoranta ne domin ya ceto ’yan kasar daga tashe-tashen hankulan siyasa da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama’a.
Tun daga juyin mulkin ne, soji sukai kane-kane a siyasar kasar. A bangare guda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da tilasta wa wasu yin kaura daga kasar.
Mista Ebren ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 1982, kuma ya mulki kasar har tsawon shekara bakwai.