Kotu ta yanke wa wanda ya kashe makwabcinsa ana dab da bikinsa hukuncin kisa

Kotun ta ce ya kashe mutumin ne ana dab da bikinsa

Kotu ta yanke wa wanda ya kashe makwabcinsa ana dab da bikinsa hukuncin kisa

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

Babbar Kotun Jihar Kwara ta yanke wa wani mutum, Mohammed Kazeem Beiwa hukuncin kisa saboda kashe makwabcinsa, Olokose Ojo Olushola.

Kotun, wacce ke zamanta a Ilorin, babban birnin Jihar, a ranar Alhamis ta ya ke hukuncin ne saboda ta ce Mohammed ya kashe Olokose ’yan kwanakin kafin ranar cikinsa a 2021.

Alkalin kotun, Mai Shari’a S.M. Akanbi, ya kuma yanke hukuncin daurin shekara 10 da biyan tarar Naira dubu 100 ga sauran mutum biyun da suka hada baki da wanda ya yi kisan, Madu Jeremiah da Mohammed Chatta.

Sai dai kotun ta saki mutum na hudu da ake zargi saboda gamsasshiyar hujjar da za ta nuna akwai hannunsa a ciki.

Lauyoyi masu shigar da kara karkashin jagorancin Babban Lauya Jihar kuma Kwamishinan Shari’a Ibrahim Sulyman, Mohammed ya sace marigarin ya boye shi a gidansa, daga bisani kuma ya kashe shi.

Lauyan ya kuma ce mutumin bayan ya sace marigayin ya kashe shi ya kuma yi gunduwa-gunduwa da ita, sai ya nemi kudin fansa duk da ya san ya riga ya kashe shi.

Masu shigar da karar dai sun gabatar da shaidu tara da kuma hujjoji masu yawa a gaban kotun.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Akanbi ya ce kotun ta samu mutum uku na farko da ake zargin sannan ta wanke na hudu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Tags