Kotu ta yanke wa wanda ya watsa wa budurwarsa ruwan batir daurin rai da rai
Ya watsa mata ne bayan ta ki yarda ta aure shi
Wata babbar kotu da ke zamanta a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin rai da rai.
Kotun dai ta samu mutumin ne mai suna Jide Afolayan Sunday mai kamin shekara 33 da haihuwa ne dai laifin watsa wa budurwarsa ruwan batir.
- Wahalar takardun kudade ta fara dawowa a Kano da Borno
- Ta mutu tana saduwa da saurayinta da ya sha maganin karfin maza
Alkalin kotun, Mai Shari’a Blessing Egwu, ta ce kotun ta samu wanda ake zargi ake kara da aikata laifin yunkurin kisan kai ta hanyar watsa wa budurwarsa mai suna Glory Sylvester Ita ruwan gubar ne saboda ta ki auren shi.
Kazalika, kotun ta kara masa da tarar Naira milyan 10 domin ayi wa budurwar tasa tiyatar fuskarta da fatar jikinta .
Afolayan Sunday dai zai yi zaman wakafi na rai da ran ne a gidan gyaran hali da ke Kalaba ne.
Mai Shari’a Egwu ta ce wanda ake zargi a abin da ake zargin ya yi yunkurin aikata kisan kai ba da wata kwakkwarar hujja ba.
’Yan sanda sun kuma tuhumi mutumin da yaudarar yarinyar zuwa wani otel da ke unguwar Marian a Karamar Hukumar Birnin Kalaba, da zummar za su yi hira, amma ya ɓige da watsa mata gubar.
Sun kuma ce hakan ya sa gubar ta lalata mata yatsu da fuskarta har zuwa gadon bayanta.
Dan sandan ya ci gaba da cewar, “Saboda zafin asid din, ɗaya daga cikin kunnuwanta ya samu matsala ta kurumta.
“Lokacin da aka kama shi ya musanta aikata laifin, amma da aka zurfafa bincike an gano shi ne wanda ya watsa mata asid din.”