Kotu ta yanke wa wata mata tarar Naira 22,680 saboda ta ki yi wa danta kaciya

Wata kotun addini ta yanke wa wata tarar Dala 140 saboda ta ki yi wa danta kaciya, don haka aka bata zabi ko dai ta yi masa kaciyar ko kuma ta biya tarar NIS 500 wanda ya yi daidai da Dalar Amurka 140, wato daidai da Naira Dubu 22, 680.Wannan mata da jaridu ba su […]

Kotu ta yanke wa wata mata tarar Naira 22,680 saboda ta ki yi wa danta kaciya
Kotu ta yanke wa wata mata tarar Naira 22,680 saboda ta ki yi wa danta kaciya

Wata kotun addini ta yanke wa wata tarar Dala 140 saboda ta ki yi wa danta kaciya, don haka aka bata zabi ko dai ta yi masa kaciyar ko kuma ta biya tarar NIS 500 wanda ya yi daidai da Dalar Amurka 140, wato daidai da Naira Dubu 22, 680.
Wannan mata da jaridu ba su ambaci sunanta ba, ta bayyana cewa ba ta son ta cutar da danta, don haka ta ki yi masa kaciya.
Wani masanin shari’a, Shimon Yaakobi da ke bai wa kotun addinin shawara, cewa ya yi, “wannan matakin da aka dauka ba a kan dokar adini aka aiwatar da shi ba. An yi hakan ne don baia wa kananan yara ’yan kasar kariya, ta yadda danta ba zai bambanta da sauran yara ba.”
Ya ce  wannan shi ne karo na farko da kotun adddini a Isra’ila ta hukunta wasu iyaye da suka ki yi wa dansu kaciya. A shekarar da ta gabata wata  kotun dab a ta addini ba, ta yanke hukunci makamancin wannan inda ta yanke hukuncin da ke goyon bayan kaciya. Babu dai wata doka a dokokin kasar Isra’ila da ta ce dole sai an yi wa yaro kaciya.
Roni tamir, wani mai fafutikar ’yancin yakin da kaciya, ya kira wannan hukuncin kaciya da kotun addinin ta yanke a matsayin “hadari ne ga dimokuradiyya.”

Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike 

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida