Kotu ta yanke wa ’yan fashi hukuncin kisa ta hanyar rataya
Matasan su uku sun amfa laifin da aka gurfanar da su a gaban kotu a kai.
A jihar Ekiti dubun wasu ’yan fashi ta cika, inda aka kama su kuma alkali ya yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Alkalin Babbar Kotun Jihar Ekiti, Justice Abiodun Adesodun, ne ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma.
- An gurfanar da wani Uba da kaninsa kan zargin yi wa diyarsa fyade a Ekiti
- An kara farashin man fetur ta bayan fage —IPMAN
An yanke wa wadanda ake tuhuman, Oluole Edward dan shekara 49 tare da Kolawole Ojo dan shekara 39 da Kolawole Tope dan shekar 20 hukuncin ne bayan sun amsa laifinsu.
An tuhumi wadanda ake zargin ne da aikata laifin kisa tare da fashi da makami a tsakanin ranar 12 ga watan Aprilun 2017 zuwa 5 ga watan Disambar 2017 din, kamar yadda Daraktan Sashen Shigar da Kararraki na jihar, Julius Ajibare, ya shaidawa manema labarai.
Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su ne ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun karbi wayarsa kuma bayan an bibiyi wayar aka samu nasarar cafke su.
Ya kara da cewa, “Sun amsa cewa sune suka yi wa Wasiu Ayinde fashin kudi Naira Miliyan daya da dubu dari takwas da hamsin a kan hanyar Erinmu-Ayedun da ke Ekiti.”
Haka nan sun karbe N1,450,000 daga hannun Adamo Ayinde a wani fashin na daban a kan hanyar Orin-Ido da ma sauran mutane da dama.
Wannan yasa alkalin babbar kotun ya yi mafani da kundin dokar jihar ta Ekiti wajen yanke hukuncin a kansu