Kotu ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa
Wata kotun tarayya a Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da aka sameta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello. Mai shari’a Yusuf Halliru ya ce hukuncin wanda ya yi kisa shi ne a kashe shi, a don haka ya yanke mata hukuncin kisa. Tuni aka wuce da ita zuwa gidan […]
Wata kotun tarayya a Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da aka sameta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Mai shari’a Yusuf Halliru ya ce hukuncin wanda ya yi kisa shi ne a kashe shi, a don haka ya yanke mata hukuncin kisa.
Tuni aka wuce da ita zuwa gidan yari na Suleja kafin inda za ta zauna har zuwa lokacin da za a zartas mata da hukuncin.
Kawo babu tabbas ko lauyoyinta za su daukaka kara ko kuma a’a.
Tun da farko Maryam, wacce ta rinka kuka a kotun, ta yi kokarin guduwa daga wurin da wadanda ake zargi suke tsayawa, amma jami’an kotu suka dawo da ita.
Wakilin Aminiya a kotun, ya ce Maryam ta rinka cewa “Inna liLlahi wa inna iLaihi raji’un,” a yayin da lauyoyinta da ‘yan uwanta ke kokarin shawo kanta.
Wakilinmu ya kuma jiyota tana cewa “ina azumi, ina addu’a… Ya Allah?”.
Ana cikin haka ne wasu mata suka rinka hayaniya a kotu, abin da ya sa alkalin ya dan tafi hutu na wani dan lokaci kafin daga bisani ya dawo ya yanke hukunci.
Kotun ta cika makil kuma an samar da tsaro sosai a ciki da wajenta.