Kotu ta yi sammacin Yahaya Bello
EFCC ta bankaɗo wani sabon zamba da ake zargin tsohon gwamnan da ya kai har N110,446,470,089.00.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta fitar da buɗaɗɗiyar takardar sammaci tana mai neman tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya gurfana a gabanta.
Mai Shari’a Maryanne Anenih ce ta yi sammacin neman tsohon gwamnan ya halarci zaman kotun a ranar 24 ga watan Oktoba domin amsa wasu ƙarin tuhume-tuhume 16 da ake yi masa.
- HOTUNA: Gwamnan Kebbi ya raba wa sarakuna motocin alfarma
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Anambra
A cewar sammacin, tsohon gwamnan zai halarci zaman kotun domin amsa tuhume-tuhumen sannan zai gurfana ne tare da wasu mutane 2 da ake ƙarar tare.
Mai Shari’a Anenih ta umarci Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC ta wallafa sammacin a jarida mafi farin jini.
Haka kuma ta umarci EFCC ta kafe kwafin sammacin a adireshin da aka sani na Yahaya Bello da bayyanannun wurare a harabar kotun.
A ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata EFCC ta gabatar wa Babbar Kotun sabbin tuhume-tuhume 16 da suka shafi zamba da take zargin Yahaya Bello ya aikata.
Tuhume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ta shigar ta hannun lauyoyin EFCC, Kemi Pinheiro da Rotimi Oyedepo da wasu lauyoyi 7, sun ƙara haɗa Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu a matsayin waɗanda ake zargi tare da Yahaya Bello.
Lamarin dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ke ’yar wasan ɓuya da mahukunta EFCC da kuma ƙin halartar wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da suke tuhumarsa kan sace zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 80.2 a lokacin da yake riƙe da madafun iko a jihar.
A ƙunshin sabbin tuhume-tuhumen, EFCC ta bayyana cewa ta bankaɗo wani sabon zamba da ake zargin tsohon gwamnan da ya kai har N110,446,470,089.00.