Kotu ta yi umarci a rufe Gidauniyar Trump saboda zargin badakala
Za a rufe Gidauniyar Shugaban Amurka Donald Trump bayan kotu ta tuhumi iyalan Shugaban Amurka da yin watanda da kudaden da gidauniyar. Babbar mai shigar da kara ta Jihar New York Barbara Underwood ce ta bayyana haka, kuma ita ce jami’ar da za ta sa ido a kan raba kadarorin da gidauniyar ta mallaka kamar […]
Za a rufe Gidauniyar Shugaban Amurka Donald Trump bayan kotu ta tuhumi iyalan Shugaban Amurka da yin watanda da kudaden da gidauniyar.
Babbar mai shigar da kara ta Jihar New York Barbara Underwood ce ta bayyana haka, kuma ita ce jami’ar da za ta sa ido a kan raba kadarorin da gidauniyar ta mallaka kamar yadda BBC ya ruwaito.
Ta tuhumi Shugaba Trump da manyan ’ya’yansa uku da amfani da gidauniyar domin azurta kansu.
A baya-bayan nan gidauniyar ta sha musanta tuhumar da bangaren shari’a ke yi mata.
Kuma wannan na daya daga cikin manyan shari’o’in da Shugaba Trump da iyalansa ke fuskanta.
Misis Underwood ta ce za a ci gaba da gudanar da shari’ar da gwamnatin jihar take yi a kan Shugaba Trump da iyalansa uku, Donald karami da Ibanka da kuma Eric.
Yadda hukunci yake
A wata sanarwa, babbar mai shigar da karar ta ce an gano “wani shiri mai tayar da hankali na yadda ake amfani da gidauniyar domin karkatar da kudaden da take tarawa kuma kamfanonin Shugaba Trump ne ke amfana- kuma ya hada da wata haramtacciyar dangantaka tsakanin kungiyar kamfen din Shugaba Trump da gidauniyar tasa,” inji ta.
Ta kara da cewa, “Gidauniyar Trump ta zama tamkar wani asusu da kamfanonin Shugaba Trump ke amfani da shi domin biyan bukatunsu na kudi da na siyasa.”
A karkashin yarjejeniyar rufe gidauniyar, Misis Underwood ta ce bangaren shari’a ne zai raba kadarorinta ga kungiyoyin da suka cancanta, “Wadanda za su kasance sanannun kungiyoyi ne a karkashin kulawar ofishina,” inji ta.
Ta ce: “Wannan babbar nasara ce ga tsarin shari’a, domin yanzu mun tabbatar cewa shari’a za ta taka duk wanda ya taka ta. Za mu ci gaba da tabbatar da cewa doka ta hukunta Gidauniyar Trump da daraktocinta saboda laifuffukan da suka tafka.”
Har yanzu Shugaba Donald Trump da manyan ’ya’yan nasa uku ba su ce uffan kan hukuncin ba.
Amma a baya-bayan nan gidauniyar ta ce tuhumar da ake mata tana da alaka da siyasa, kuma ta zargi babbar mai shigar da karar da rike Dala miliyan 1.7 na sauran kudaden gidauniyar “saboda dalilai na siyasa.”
A watan Yunin da ya gabata ma Shugaba Trump ya fitar da wani sako a Tiwita da ke cewa ba zai mika wuya ba domin babu laifin da gidauniyarsa ta aikata.