Kotu ta yi wa mai fyade daurin rai-da-rai

Kota ta yanke wa mutum da ya yi wa ’yar shekara biyu fyade daurin rai-da-rai.

Kotu ta yi wa mai fyade daurin rai-da-rai

Kota ta yanke wa wani mutum da ya yi wa ’yar shekara biyu fyade daurin rai-da-rai.

Mai Shari’a Abiodun Akinyemi na Babbar Kotun Jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta ya ce hujjojin sun tabbatar da mutumin ya lalata yarinyar.

“Hujjojin, sun tabbatar min cewa ya lalata yarinyar kuma laifin da ake tuhumarsa da shi ya tabbata”, inji alkalin.

Musanta zargin yi wa karamar yarinyar fyade bai hana alkalin ya yanke wa matashin hukuncin daurin rai-da-rai ba a zaman kotun na ranar Talata.

Mai gabatar da kara, Misi Oluyemisi Aruleba ta shaida wa kotun cewa mutumin ya yi wa yarinyar fyade ne da karfin tsiya.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato