Kotu ta yi wa ’yan Boko Haram hudu daurin rai da rai
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin dauri rai da rai ga wasu mutum hudu da aka tuhuma da hannu a dana bama-baman da suka tashi a shekara ta 2011 a Suleja a Jihar Neja da kuma Dakna da Bwari yankin birnin tarayya. Wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da ran […]

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin dauri rai da rai ga wasu mutum hudu da aka tuhuma da hannu a dana bama-baman da suka tashi a shekara ta 2011 a Suleja a Jihar Neja da kuma Dakna da Bwari yankin birnin tarayya.
Wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da ran su ne Shu’aibu Abubakar da Salisu Ahmed da Umar Babagana da kuma Mohammed Ali.
Wadanda aka dauren an ce wakilai ne na kungiyar Boko Haram, kuma an same su da laifin samon horon sarrafa makamai ba bisa ka’ida ba da jigilar abubuwa masu fashewa da hannu a ayyyukan ta’addanci da dana bama-baman da suka jawo asarar rayukan jama’a da dama a lokacin taron siyasa da ofishin Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da ke Suleja da Dakna.
A lokacin shari’ar an shaida wa kotun cewa Abubakar da Ahmed a lokuta da dama sun sayi bama-bamai daga Azara da ke Jihar Nasarawa. Kuma kotun ta ji cewa Babagana da Ali sun raka Abubakar lokacin da yake jigilar bama-baman zuwa Kano don ayyukan ta’addanci kafin sojoji su kama su a Kachiya da ke Jihar Kaduna.
Abubakar, wanda ya musanta cewa kayayyakin na ayyukan ta’addanci ne ya shaida wa kotun cewa zai yi amfani da su ne don hakar ma’adinai dukmda cewa bai samu wurin da zai haka ba.
Sai dai kotun ta ce mai gabatar da kara ya kawo gamsassun hujjojin cewa an samu Abubakar da bama-bamai kuma yana jigilarsu ne don ayyukan ta’addanci. Kotun ta ce, “Wurin da ake hakar ma’adinan na Azara ne inda aka sayo kayayyakin. Abin tambaya me ya sa aka dauke kayan daga inda ake hakar ma’adanin?”
Kotun ta ce Abubakar ya gaza kawo wata ingantacciyar amsa kan dalilin jigilar kayan a tsakiyar dare kafin a kama shi.
Babagana da Ali kuma sun ce ba su da masaniyar abin da Abubakar yake jigila, amma hujjojin da aka gabatar gaban kotun sun tabbatar da cewa akwai rahoton sirri da ya nuna cewa ’yan ta’adda suna jigilar bama-bamai a daren da aka kama su.
Baya ga haka kotun ta ce gudun da Ali ya yi bayan sojoji sun dakatar da su ya nuna ya san abin da ke cikin motar.
Tun farko lauyoyin wandanda ake tuhuma, Kebin Okoro da Nuraini Sulyman, sun roki kotun ta yi musu sassauci, amma lauya mai gabatar da kara Thompson Olatigbe ya nemi kotun ta yi musu daurin rai da rai.
Olatigbe ya ce “Wadanda aka hukuntan wakilan kungiyar Boko Haram ne, wata kungiyar ta’adda da ta halaka dalibai 24 kwanan nan. Don haka ina bukatar kotun ta yi musu daurin rai da rai domin zama darasi ga masu sha’awar ta’addanci.”
Da take yanke hukunci alkalin kotun Mai shari’a Bilkisu Aliyu ta ce, “Wadannan masu laifi sun yi amfani da nakiyar fasa duwatsu da hakar ma’adinai kan ’yan uwansu mutane ba tare da sun yi musiu komai ba. Ran dan Adam na da martaba, kuma ba wata rai da ta fi wata. Masu laifin sun nuna tsabagen rashin ganin girman rayuka, wannan mafi munin hali ne kuma sun cancanci a raba su da jama’a. don haka an yanke hukunci daurin rai da rai ga mai laifi na daya zuwa na hudu.”
Kotun ta kuma yi daurin shekara 10 ga Umar Ibrahim dan uwan Bashir Madalla daya daga cikin shugabannin kungiyar da horar da wasu daga cikin wadanda aka hukunta yadda ake sarrafa bindiga don daukar fansar kashe wakilansu a jihohin Borno da Yobe, saboda zama dan aikensa. Sannan ta sallami usa Adamu, saboda babu shaidar da za ta nuna alakarsa da tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Mai shari’a Bilkisu ta ce mota kirar Honda Cibic da aka yi amfani da ita a matsayin shaida za a mika ga Gwamnatin Tarayya, yayin da shaida ta biyu nakiyoyi 200 da daurin wayoyi biyu da aka gabatar za a mika su ga hukumomin da suka dace don lalata su bayan karewar wa’adin daukaka kara.