Kotu ta yi watsi da ayyana kungiyar Palasdinawa a matsayin ’yar ta’adda

Kotun Daukaka Kara ta Birtaniya ta yanke, bayan gwamnatin kasar ta daukaka kara tana neman soke hukuncin Babbar Kotun kasar wadda tun da farko ta yanke hukunci cewa matakin da gwamnatin ta dauka ya saba da wa doka.

Kotu ta yi watsi da ayyana kungiyar Palasdinawa a matsayin ’yar ta’adda

Kotun Daukaka Kara ta Birtaniya ta yi watsi da haramcin da gwamnatin kasar ta kakaba wa kungiyar rajin Palasdinawa ta Palestine Action a matsayin ’yar ta’adda.

A ranar Litinin ne Kotun Daukaka Kara ta Birtaniya ta yanke, bayan gwamnatin kasar ta daukaka kara tana neman soke hukuncin Babbar Kotun kasar wadda tun da farko ta yanke hukunci cewa matakin da gwamnatin ta dauka ya saba da wa doka.

Babbar Kotun Birtaniya ta bayyana cewa dokar haramta kungiyar da gwamnatin Birtaniya ta yi a karkashin Dokar Yaki da Ta’addanci na 2000, ya saba da tanadin dokar kasar kuma zalunci ne.

Da take karanta da hukunci, Babbar Alkalin Kotun, Sue Carr, ta bayyana cewa, kotun ta “Cim ma matsaya cewa haramta kunciyar babu adalci kuma don haka muka amince wa Sakatare Harkokin Cikin Gida ya daukaka kara kan hukuncin karamar kotun.

Gwamnatin Birtaniyya ta kama mutane akalla 1,600 masu alaka da kungiyar Palestine Action, tun bayan da gwamantin ta ayyana kungiyar a matsayin ’yar ta’adda.

A yayin zaman na watan Afrilu, lauyoyin Mininstan Cikin Gida na Birtaniya, Shabana Mahmood, sun yi jayayya da matsayar kotun cewa haramta kungiyar yana da mummunan tasiri ga ’yancin fadar albarkacin baki.

Amma daya daga cikins shugabannin da suka kafa kungiyar, Huda Ammori, ta bayyana cewa haramcin ya “dakile ’yancin fadin albarkacin baki da kuma gudanar da taruka ga dimbin mutane masu goyon bayan Palasdinu.”

Mai Shari’a Carr ta bayyana cewa irin wadannan haramci “ciki suke da rudani” tana mai karawa da cewa “babban kuskure ne rashin yin la’akari da cewa kungiyar Palestine Action tana goyon bayan tashin hankali, wanda kan iya kaiwa ga ta’adanci.”

A cewar Carr, gangamnin da Palestine Action ta gudanar “an yi shi ne da nufin rufe wuraren kasuwancin da doka ta amince da su”, inda ya ƙara da cewa “barazanar gaba da haɗarin da Palestine Action za ta iya haifarwa ga wasu mutane da dukiyoyinsu na iya zama muhimman abubuwan da za a yi la’akari da su”.

A kan haka ne, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Ammori ta ce za ta “yi gwagwarmaya kan haramta ƙungiyar har zuwa Kotun Koli da Kotun Turai ta Kare Haƙƙin Dan Adam” domin kifar da “ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi tsananta kan ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin yin zanga-zanga a tarihin Biritaniya na zamani.

Jami’ar Bayero ta Kano ta kori ɗalibai 78

Kotu ta yi watsi da ayyana kungiyar Palasdinawa a matsayin ’yar ta’adda

Wata matar aure ta sari mijinta da adda 

Lakurawa sun kashe fararen hula 20 a Kebbi