Kotu ta yi watsi da bukatar rage shekarun dan 69 da shekara 20

Wani dan kasar Netherland mai suna Emile Ratelband mai shekara 69, da ya bayyana cewa, shekarunsa na kawo masa tangarda wajen neman aiki da kuma yin soyayya, kuma ya bukaci kotu ta rage yawan shekaruna da shekara 20 ya gaza samun nasara. Wata kotun Netherland ta yi watsi da bukatar Emile Ratelband na rage shekarunsa […]

Kotu ta yi watsi da bukatar rage shekarun dan 69 da shekara 20

Wani dan kasar Netherland mai suna Emile Ratelband mai shekara 69, da ya bayyana cewa, shekarunsa na kawo masa tangarda wajen neman aiki da kuma yin soyayya, kuma ya bukaci kotu ta rage yawan shekaruna da shekara 20 ya gaza samun nasara.

Wata kotun Netherland ta yi watsi da bukatar Emile Ratelband na rage shekarunsa da shekara 20 don ya jawo hankalin duniya.

A karshen watan jiya ne, Emile Ratelband ya bukaci kotun Arnhem  ta canja shekarun haihuwarsa zuwa shekara 49, inda ya ce, shekarun haihuwarsa na asali ba su nuna asalin abin da zai iya gudanarwa wanda hakan yana sanya shi wahala kafin ya samu aikin yi da kuma yin soyayya.

Emile ya ce, a jikinsa bai jin cewa, shi dan shekara 69 ne don haka yake bukatar wasu hanyoyin da za a amince wa bukatarsa ta rage shekarunsa a duniya, musamman tunda akwai ’yancin canja suna da jinsi.

A yayin da kotun take sauraren karar a ranar Litinin ta ce, dokar kasar ta tanadi ’yanci da abin da ya wajaba ga dan kasa a kan tsarin shekaru kamar: ’yancin kada kuri’a da kuma shiga makaranta. To idan har za a biya wa Emile bukatarsa, wannan dokar ba ta da ta wani amfani ke nan inji kotun.

Kamfanin Dillancin Labarai na Rueters ya ce kotun ta ce, Mista Emile na da ’yancin yin rayuwa kamar dan shekara 20 yadda yake so, amma canja takardun shaidar haihuwarsa zai lalata bayanansa na shekara 20 har zuwa rajistar haihuwarsa da aurensa da kuma rijistar hadin gwiwa, wanda canzawar za ta haifar da wani abu da doka ba ta tanadar ba tare da kawo illa ga al’umma.

Kotun ta amince jama’a su ci gaba da rayuwarsu cikin koshin lafiya don su samu tsawon rai, amma ba ta amince da canja rage shekarun mutum don ya ji shi matashi ne ba.

Kotun ta ce, Emile ya gaza gamsar da kotun kan kalubalen da yake fuskanta na a yawan shekaru. Emile, ya fahimci kotun ba za ta biya masa bukatarsa don haka ya yi yunkurin daukaka kara. Saboda kotun duk ta bayar da matakan da za a bi idan an daukaka karar. Kuma ya ce, yana daya daga cikin mutane na farko a dubban jama’ar da suke son canja shekarunsa ta hanyar bin ka’ida.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo