Kotu ta yi watsi da dokar Majalisar Jihar Nasarawa ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi

Babban Kotun Jihar Nasarawa ta Uku da ke Lafiya ta yi wasi da wata doka da Majalisar Dokokin Jihar ta kafa inda ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar daga shekara biyu zuwa daya. Alkallin Kotun Mai shari’a A’isha Ahmed wadda ta jagoranci zaman kotun a ranar Litinin da ta gabata ta ce majalisar ba […]

Kotu ta yi watsi da dokar Majalisar Jihar Nasarawa ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi
Kotu ta yi watsi da dokar Majalisar Jihar Nasarawa ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi

Babban Kotun Jihar Nasarawa ta Uku da ke Lafiya ta yi wasi da wata doka da Majalisar Dokokin Jihar ta kafa inda ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar daga shekara biyu zuwa daya.
Alkallin Kotun Mai shari’a A’isha Ahmed wadda ta jagoranci zaman kotun a ranar Litinin da ta gabata ta ce majalisar ba ta bi ka’ida ba wajen kafa dokar inda ta yanke hukuncin cewa shugabannin kananan hukumomin su ci gaba da gudanar da mulkinsu har na shekara biyu.
Wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Lafiya dauke da sanya hannun lauyar shugabannin kananan hukumomin Barista Mary Onyeka ta ce “Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya Majalisar Dokokin Jihar nan ta kafa wata doka da ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar nan daga shekara biyu zuwa daya wanda hakan ya sa shugabannin kananan hukumomin suka je kotu don kalubalantar dokar. Kuma bayan gudanar da bincike mun gano cewa majalisar ba ta bi hanyoyi da suka dace ba wajen rage wa’adin shugabannin, kuma bayan sauraran shari’ar Mai shari’a A’isha Ahmed ta umarci majalisar ta bar shugabannin kananan hukumomin su ci gaba da gudanar da aikinsu har sai wa’adin shekara biyunsu ya kare kamar yadda aka saba a jihar nan.”
Barista Mary Onyeka ta kara da cewa idan majalisar ta ki bin dokar kotun za su garzaya zuwa kotu ta gaba don tabbatar an yi aiki da umarnin.