Kotu za ta daura wa bazawara aure saboda mahaifinta ya gudu

Wata bazawara mai kimanin shekara 27 mai suna Maryam Habu daga kauyen Kwarra a karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa ta gurfanar da mahaifinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Dutes, bisa yi mata auren dole da mijin da ba ta so, inda mahaifin nata maisuna Malam Habu ya gudu zuwa Legas.  Ana zargin Malam […]

Kotu za ta daura wa bazawara aure saboda mahaifinta ya gudu
Kotu za ta daura wa bazawara aure saboda mahaifinta ya gudu

Wata bazawara mai kimanin shekara 27 mai suna Maryam Habu daga kauyen Kwarra a karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa ta gurfanar da mahaifinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Dutes, bisa yi mata auren dole da mijin da ba ta so, inda mahaifin nata maisuna Malam Habu ya gudu zuwa Legas. 

Ana zargin Malam Habu da karbar Naira dubu takwas daga wajen wanda ’yarsa take so da aure amma ya ki aurar masa da ita, kuma ya hana ’yan uwansa daura mata aure da shi, inda ya bar garinsu aka neme shi aka rasa.
Wakilimmu ya samu labarin cewa yarinyar ta girma ne a gaban mahaifiyarta da ba su tare da mahaifinta, kuma irin wannan kama-karya mahaifinta ya yi ya aurar da ita ga wanda ba ta so, kuma bayan auren ya mutu ne yake son sake yi mata kama-karya don aurar da ita ga wanda ba shi take so ba, alhali ta gabatar masa da wanda take so har ya amshi kudin na-gani ina-soNaira dubu takwas a wajensa yana shirin turo magabatansa amma sai aka nemi mahaifin aka rasa daga bisani ne aka samu labarinsa a Legas.
Bazawarar ta shaida wa Alkalin Kotun Mai sharia Jibril Muhammed cewa mahaifinta ya hana ta yin aure kuma ya yi barazanar cewa duk wanda ya daura mata aure da wanda take so bayan baya nan idan ya dawo zai yi kararsa a kotu.
Bayan sauraren bazawarar ce, sai Mai shari’a Jibril ya ce kotun za ta daura mata aure bayan ta samu ganawa da kakanta da ya haifi mahaifinta, kuma ya umarci ’yan sanda a duk inda suka ga mahaifin bazawarar su kama shi su mika shi su tsare kuma su sanar da da shi domin daukar mataki a kansa.