Kotu zata ci gaba da sauraran karar bidiyon Ganduje ranar 21 ga Nuwamba
Babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 21 ga Nuwamba, 2018 don ci gaba da sauraran karar da wata Kungiyar lauyoyi ta shigar akan binciken da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano suke yi wa Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje na zarginsa da karbar cin hanci a wani bidiyo da aka fallasa. Kungiyar lauyoyin sun shigar […]
Babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 21 ga Nuwamba, 2018 don ci gaba da sauraran karar da wata Kungiyar lauyoyi ta shigar akan binciken da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano suke yi wa Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje na zarginsa da karbar cin hanci a wani bidiyo da aka fallasa.
Kungiyar lauyoyin sun shigar da karar gaban alkali Ahmed T.Badamasi don tuhumar kwamitin mutum bakwai da majalisar ta kaddamar da nufin yin binciken lamarin.