Kotun Ƙoli: Kwankwaso ya jagoranci addu’ar roƙa wa Abba nasara

Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron addu’a na musamman a gidansa da ke Kano da safiyar Litinin.

Kotun Ƙoli: Kwankwaso ya jagoranci addu’ar roƙa wa Abba nasara

Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron addu’a na musamman a gidansa da ke Kano da safiyar Litinin.

An gudanar da addu’ar ta musamman ce domin rokn nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a shari’ar zaben gwamnan Kano da ake Kotun Ƙoli.

Addu’ar da wata kungiyar ta Musulunci – Mu’assasatul Kwankwasiyya ta shirya ta gudana karkashin jagorancin Malam Yahaya Sufi, Malam Ashiru Nata’ala, Malam Bazallahi Nasiru Kabara da Malam Sadiq Isiyaku Rabi’u.

A yayin da suke gudanar da addu’o’in, Malaman sun yi addu’ar Allah ya ba Abba Kabir Yusuf nasara a kotun koli da kuma Allah ya ba wa jihar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Taron addu’ar ya samu halartar jami’an Gwamnatin Abba Kabir Yusuf da masu rike da mukaman siyasa da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne kotun koli karkashin jagorancin wasu alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ta kebe hukuncin bayan sauraron lauyoyin da ke kan lamarin.

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu

‘Yar China na fuskantar saki bayan ta haifi jariri baƙar fata

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga