Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP

Kotun ta sake dawo da Anyanwu a matsayin halastaccen sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.

Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP

Kotun Ƙoli ta yanke hukunci tare da tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin halastaccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa.

Anyanwu, wanda na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya shafe lokaci yana takun-saƙa da Sunday Ude-Okoye kan wannan matsayi.

Ude-Okoye ya samu goyon bayan wasu ɓangarori na jam’iyyar PDP bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu ta tabbatar da naɗinsa, biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tsige Anyanwu.

Sai dai, a ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalan Kotun Ƙoli guda biyar, ya yanke hukunci cewa rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya al’amari ne na cikin gida, kuma ba hurumin kotu ba ne sai dai idan akwai wasu dalilai na musamman.

Mai shari’a Jamilu Tukur, wanda ya jagoranci hukuncin, ya bayyana cewa irin wannan shari’a za ta iya shiga hurumin kotu ne kawai idan ta ƙunshi karya doka, aikata laifi, ko saɓa wa yarjejeniya.

Rigima game da muƙamin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa, ta samo asali ne bayan Anyanwu ya ajiye muƙamin don yin takarar gwamna a Jihar Imo, amma bai samu nasara ba.

Yunƙurinsa na sake dawowa kan muƙamin ya jefa jam’iyyar cikin ruɗani.

Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da tsige shi a watan Disamban 2024, Anyanwu ya shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, wacce a yanzu ta yanke hukunci, tare dawo da shi a matsayin halastaccen sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.