Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na Bauchi

Kotun ta kori ƙarar da Sadique Abubakar na jam’iyyar APC ya ɗaukaka.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed. (Hoto: Ttwitter.com/SenBalaMohammed)

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan Jihar Bauchi.

Babbar Kotun ta kori ƙarar da Sadique Abubakar na jam’iyyar APC ya ɗaukaka saboda rashin cancanta.

Ana iya tuna cewa, Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara duk sun tabbatar da nasarar gwamnan, amma tsohon babban hafsan sojin saman Najeriyar ya garzaya Kotun Ƙolin kuma hakarsa ba ta cimma ruwa.

Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe a shari’ar da ake yi ta tantance ingancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen na watan Maris.

Bala Mohammed ya lashe zaɓen ne a ƙoƙarin sa na neman karo na biyu na mulkin da ya fara a a watan Mayun 2019.