Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Legas Sanwo-Olu

Duk kotuna uku sun tabbatar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Legas.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Legas Sanwo-Olu

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Babajide Sanwo Olu a matsayin halastaccen gwamnan Jihar Legas.

Alƙali Garba Lawal ne ya gabatar da hukuncin, yana mai korar ƙarar da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour ya ɗaukaka saboda rashin cancanta.

Sauran alkalan, wadanda suka hada da mai shari’a Inyang Okoro da Emmanuel Agim da Uwani Abba-aji da Adamu Jauro suna karanto hukuncin na bai ɗaya da cewa ita kanta takardar ɗaukaka karar wulakanci ne ga tsarin kotu.

Tun a watan Satumbar bara ne Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Legas ta tabbatar da nasarar Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen gwamna.

Daga bisani, kuma Kotun Daukaka Kara ta sake tabbatar masa da nasara, inda a yanzu dukkanin kotunan uku suka halasta masa zama Gwamna Legas.