Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Kogi da Bayelsa

Kotun Ƙolin ta yi fatali da hujjojin da masu ƙalubalantar nasarar gwamnonin suka gabatar

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Kogi da Bayelsa

Kotun Kolin Najeriya (Hoto: Onyekachukwi Obi)

Kotun Ƙolin Nijeriya da ke Abuja, babban birnin ƙasar, ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa.

A hukuncin da ta yanke ranar Juma’a Kotun ta tabbatar da Sanata Duoye Diri na jam’iyyar PDP, a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Bayelsa.

Wannan na zuwa ne bayan kotun ta yi watsi da ƙarar da Timipre Silva na jam’iyyar APC, ya shigar gabanta yana ƙalubalantar nasarar da Mista Diri ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Haka ma kotun ta tabbatar da nasarar Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Kogi, bayan watsi da ƙorafin Murtala Ajaka na jam’iyyar SDP.

Kotun ta ce ta tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, wadda ta tabbatar da Ododo.

A dai ranar Juma’ar ne kuma Kotun Ƙolin ta tabbatar da nasarar Gwamnan Imo, Hope Uzodinma a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kotun wadda Mai Shari’a Sadiq Umar ya jagoranci karanto hukunce-hukuncen, ta tabbatar da nasarar Uzodinma ne bayan fatali da ƙorafin ɗan takarar jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, saboda rashin gamsassun hujjoji.