Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano

Kotun na dakon hukuncin kotun ƙoli kafin ta zartar da nata hukuncin.

Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba.

Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar.

Ya jaddada cewa kawai Kotun Ƙoli ce ke da ikon sauya hukuncin mayar da Sanusi kan karagar mulki.

“Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke hukuncinta na baya ba. Kawai dai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe,” in ji Dederi yayin da yake magana da manema labarai.

Ya ƙara da cewa kotun ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar na da hurumin dawo da Sanusi kan sarautar Kano.

“Hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga watan Janairu ya tabbatar da cewa Kotun Tarayya ta farko ba ta da ikon yanke hukunci kan wannan batu.

“Sanusi na nan a matsayin Sarki har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci,” in ji shi.

Shari’ar ta samo asali ne bayan Aminu Baba DanAgundi, ɗaya daga cikin magoya bayan tsohon Sarki Aminu Ado Bayero, ya garzaya kotu tare da ƙalubalantar dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Jihar.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci cewa komai zai ci gaba da kasancewa yadda yake har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin.