Kotun Ɗaukaka Ƙara ta mayar wa Muhuyi Magaji muƙaminsa
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta rushe dakatarwar da aka yi wa Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji daga kan muƙaminsa. A hukuncin da alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar suka yanke, sun bayyana dakatarwar da aka yi wa Muhuyi Magaji a matsayin take haƙƙinsa. […]
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta rushe dakatarwar da aka yi wa Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji daga kan muƙaminsa.
A hukuncin da alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu ta zartar suka yanke, sun bayyana dakatarwar da aka yi wa Muhuyi Magaji a matsayin take haƙƙinsa.
- Kashi 70 na ’yan Najeriya da aka bai wa cin hanci a shekarar 2023 sun ƙi karɓa — ICPC
- Yadda bikin Ranar Shan Fura ta Duniya zai gudana
Da yake yanke hukuncin a ranar Juma’a, Mai Shari’a Fadawu ya bayyana cewa, “dakatarwar da Kotun Da’ar Ma’aikata ta yi Muhuyi ba ta dace ba kuma ta saɓa wa tsarin jin ba’asin ko wane ɓangare. Kuma mun umarci a miƙa batun ga wani rukunin alƙalan Kotun Da’ar Ma’aikata na daban.”
Ana iya tuna cewa a ranar 4 ga watan Afrilun 2023 aka dakatar da Muhuyi Magaji, sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba da kotun da’ar ma’aikatan ke yi masa.
Tun a wancan lokacin ne Kotun Da’ar Ma’aikata, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar, ta umarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da Sakataren Gwamnatin jihar su naɗa wanda zai jagoranci hukumar yaƙi da cin hancin a mataki na riƙo har sai an kammala sauraron ƙarar.