Kotun Abuja ta daure Balabane rai da rai kan zargin ta’addanci
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani dan kasar Lebanon mai suna Taha Roda bisa samunsa da ayyukan ta’addanci, bayan da aka kama shi da dimbin makamai a Kano.Hukumar Tsaron kasa (SSS) ce ta gurfanar da Taha a gaban kotu tare da wasu mutanen Lebanon uku […]
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani dan kasar Lebanon mai suna Taha Roda bisa samunsa da ayyukan ta’addanci, bayan da aka kama shi da dimbin makamai a Kano.
Hukumar Tsaron kasa (SSS) ce ta gurfanar da Taha a gaban kotu tare da wasu mutanen Lebanon uku da suka hada da Mustapha Fawaz da Abdullah Thani, wadanda kotun tta wanke daga zargin hannunsu a ayyukan ta’addancin.
Malam Fawaz abokin hadin gwiwa ne na shagon kasuwanci mafi girma a Abuja da ake kira Amigo Supermarket da kuma lambun shakatawa na Wonderland Amusement Park, shi ma da ke Abuja.
Dukkan gine-ginen biyu an rufe su tun lokacin da sojoji da jami’an SSS suka kama wadanda ake zargin. A ranar 21 ga Oktoba kotun ta gaza yanke hukunci kan lamarin bayan da alkalin kotun Mai shari’a Adeniyi Ademola ya jingine yanke hukuncin lokacin da lauyoyin bangarorin biyu suka kammala bayar da bayanansu.
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da wadanda ake zargi, Mustapha Fawaz da Abdallah Thahani da kuma Talal Ahmed Rodo, a kotun ne bisa zargin aikata ayyukan ta’addanci da suka hada da shigo da makamai ta haramtacciyar hanya.
Sojoji ne suka gano dimbin makamai a wani gini da ake zargin na wani mutumin Lebanon ne a Kano. Kuma nan da nan mahukuntan Najeriya suka rufe Amigo Supermarket da Wonderland Amusement Park na su Malam Fawaz.
An zargi mutanen Lebanon din da kasancewa ’ya’yan kungiyar Hezbollah, wata kungiya da ke kasar Lebanon da Amurka ta sanya ta cikin kungiyoyin ’yan ta’adda.
A yayin shari’ar lauya mai gabatar da kara Simon Egede ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi musamman lura da shaidun da aka gabatar. Mista Egede ya ce Hezbollah kungiya ce ta ’yan ta’adda kuma haka ya kamata a dauke ta. Ya ce duk wata kungiya da take da hannu a tashin bama-bamai da rusa abubuwa kungiya ce ta ’yan ta’adda, don haka ya roki kotun ta hukunta wadanda ake zargin.
Sai dai lauyan kariya Robert Clarke (SAN) ya ki amincewa da bukatar lauyan masu karar, inda ya ce gwamnatin Najeriya ba ta bayyana Hezbollah a matsayin kungiyar ta’adda ba. Ya ce Hezbollah kungiya ce kamar kowace kungiya, inda ya roki kotun ta wanke tare da sallamar wadanda ake tuhumar.