Kotun Amurka ta samu Trump da laifin tayar da rikicin zabe

Sai dai Trump ya yi watsi da hukuncin

Kotun Amurka ta samu Trump da laifin tayar da rikicin zabe

Trump lokacin da ya bayyana a gaban kotu a Manhattan

Wata kotun Amurka da ke birnin Georgia ta samu tsohon Shugaban Kasar, Donald Trump da laifin yunkurin tayar da tarzoma bayan ya fadi zaben kasar a 2020.

Wannan ne dai karo na hudu da kotuna suke samun Trump da hannu a aikata laifukan da ake zarginsa da su daban-daban.

An dai samu Trump ne tare da wasu mutum 18 da aka tuhume su tare da aikata laifuka 41 masu alaka da tayar da zaune da nufin soke nasarar da Shugaba mai ci, Joe Biden ya samu a zaben.

Hukuncin dai mai shafuka 98 ya nuna cewa wadanda ake tuhumar za su iya fuskantar hukuncin daurin shekara 20 a gidan kaso.

Wannan dai shi ne yanke hukunci mafi tsauri a cikin dukkan wadanda ake yi wa tsohon Shugaban. Yanzu haka kuma yana fuskantar wata tuhumar a biranen New York da Washington DC da kuma Florida a wasu tuhume-tuhumen guda uku daban-daban.

Sai dai Trump ya yi watsi da hukuncin, inda ya bayyana shi a matsayin bi-ta-da-kulli.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta mai suna Truth, Trump ya ce nan da mako mai zuwa “zan wallafa cikakken bayani kan ainihin abin da ya faru wanda sam babu cikakkiyar hujja kan ainihin abin fda ya faru a Georgia a 2020.”

“La’akari da abin da wannan rahoton da bai kammala ba ya nuna, ya kamata a yi watsi da shi. Za mu fitar da ainihin abin da zai kare mu,” in ji tsohon Shugaban na Amurka.