Kotun Bangladesh ta tuhumi yaro dan shekara biyu

A kasar Bangladesh, a wani gari mai suna Comapnyganj, da ke yankin Sylhet, an kama wani yaro dan shekara biyu, a matsayin mai lafin da ake tuhuma da sayar da man girki gurbatacce. Jami’in duba gari Shamsuddeen, wanda ya kai farmaki wani katafaren shagon sayar da kaya na Aftab Store, a kasuwar Shah Arefin Bazaar […]

Kotun Bangladesh ta tuhumi yaro dan shekara biyu
Kotun Bangladesh ta tuhumi yaro dan shekara biyu

A kasar Bangladesh, a wani gari mai suna Comapnyganj, da ke yankin Sylhet, an kama wani yaro dan shekara biyu, a matsayin mai lafin da ake tuhuma da sayar da man girki gurbatacce. Jami’in duba gari Shamsuddeen, wanda ya kai farmaki wani katafaren shagon sayar da kaya na Aftab Store, a kasuwar Shah Arefin Bazaar da ke kauyen Noakut, inda ya samu gurbataccen man girki a wani shago mai suna Aftab Store. Jami’in ya kama wani karamin yaro mai suna Aftab Ali, wanda yake tuhuma da laifi a matsayinsa na mai shago, don haka ya danka shi a hannun hukuma.
Da hukuma ta samu wannan mummunan labara, na rahoton da aka kai kan Aftab Ali, sai kawai ta sanya jami’an tsaro suka kama yaro suka tsare shi. Jaridar The Daily Star ta kasar Bangladesh, ta bayyana cewa Lauyan Kantin Aftab, Ashok Kar, ya bayyana wa wakilin jaridar cewa, ‘wannan jami’in dubari bai yi kyakkyawan bincike ba, tunda lasisin izinin gudanar da hada-hadar kasuwanci na wannan shago mallakar mahaifin yaron, mai suna Intaj Ali.’
Kotun da aka gurfanar da wannan karamin yaro ta bayar da belinsa, amma bayan da hukuma ta tsare shi, kuma hukumar shari’a ta bincike shi. Sai dai lauyan ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, kotu za ta fitar da yaon daga cikin wannan badakalar shari’a. “Abin takaicin kawai shi ne an kyale wannan jami’in duba gari yana yawo ba tare da an hukunta shi ba,” inji shi. Domin a cewarsa, sabuwar dokar kare hakin yara, wanda aka amince da ia, ta yi nuni da cewa duk anda ya bayar da bayanan karya a kan ananan yara, wadanda hukuncin doka bai hau kansu, dole ne kotu ta hukunta shi.
Doka ta tanadi tarar Tk dubu 25 (kudin Bangladesh) ko fiye da haka akan duk wanda ya saba mata. Kuma idan mutum a kasa biya, a cewar lauyan, to zai yi zaman kurkuku na shekara shida.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan