Kotun Birtaniya ta wanke Diezani Alison-Madueke daga zarge-zargen cin hanci
An shafe sama da shekaru 10 ana tuhumar Diezani game da zargin cin hanci.
Wata Kotu a Birtaniya ta wanke tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkanin tuhume-tuhumen cin hanci guda shida, lamarin da ya kawo ƙarshen shari’ar da ta ɗauki tsawon shekaru sama da 10.
Kotun Southwark Crown ta yanke hukuncin ne bayan alƙalai sun shafe sa’o’i sama da 46 suna nazari a kan shari’ar.
- Ce-ce-ku-ce ya ɓarke tsakanin Davido da Rarara kan matsalar tsaro a Najeriya
- ’Yan majalisa sun nemi Tinubu ya magance matsalar tsaro ko ya sauka daga kan mulki
Masu gabatar da ƙara sun zarge ta da karɓar cin hanci daga kamfanonin mai da iskar gas domin ba su kwangiloli a lokacin da take minista tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
Sannan sun ce tana rayuwa ta alfarma da kuɗaɗen haram.
Sai dai Diezani ta musanta dukkanin zarge-zargen, tana mai cewa ba ta taɓa karɓar cin hanci ba, kuma ba ta da iko kai-tsaye a kan rabon kwangiloli.
Lauyoyinta sun bayyana cewa kuɗaɗen da aka nuna a shari’ar na ayyukan gwamnati ne ko na ƙashin kanta, ba na haram ba.
Hakazalika, kotun ta wanke sauran waɗanda ake tuhuma guda biyu, ciki har da wani jami’in harkar mai, Olatimbo Ayinde, da kuma ɗan uwanta, Doye Agama, waɗanda aka zarga da hannu a shari’ar.
Lauyoyinta sun ƙara da cewa Diezani ta samu kwanciyar hankali bayan wannan hukunci, musamman duba da cewar ta shafe shekaru 11 ana binciketa.
Sun ce shari’o’in sun jefa ta da iyalanta cikin matsanancin hali.
Kawo yanzu, masu gabatar da ƙara na Birtaniya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da hukuncin kotu ba.