Kotun CCT zata ci gaba da sauraran karar Onnoghen ranar Litinin

Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta sanar da ranar 4 ga watan Faburairu 2019 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraran shagri’ar Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Samuel Onnoghen da ake tuhuma da rashin bayyana kadarorinsa. Wannan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke ne a Abuja a ranar […]

Kotun CCT zata ci gaba da sauraran karar Onnoghen ranar Litinin

Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta sanar da ranar 4 ga watan Faburairu 2019 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraran shagri’ar Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Samuel Onnoghen da ake tuhuma da rashin bayyana kadarorinsa.

Wannan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke ne a Abuja a ranar Laraba inda ta yi watsi da bukatar Babban Jojin na a hana Kotun Da’ar Ma’aikatan yi masa shari’a.

Kakakin Kotun CCT, Ibraheem Al-Hassan ya shaida wa wakilinmu cewa Alkalin Kotun CCT, Danladi Umar yana sane da hukuncin Kotun Daukaka Karar wanda yake nufin kotunsu ta ci gaba da shari’ar.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta