Kotun Daukaka Kara ba ta yi min adalci ba — Gwamnan Filato
A ranar Talata ne ake sa ran za a saurari takaitaccen bayanin Gwamna Mutfwang a Kotun Koli.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang, ya shaida wa Kotun Koli jiya Alhamis cewa, Kotun Daukaka Kara ba ta yi masa adalci ba wajen soke zabensa.
Mutfwang ya bayyana hakan ne a cikin ƙunshin bayanan da ya miƙa wa Kotun Koli batutuwa takwas da ya gabatar wa Kotun Daukaka Kara domin tabbatar da sahihancin zabensa, sai dai ya ce daga ciki, daya ne kawai aka tantance.
Ana iya tuna cewa, a ranar 19 ga watan Nuwamba 2023 ne kwamitin mutane uku na Kotun Daukaka Kara karkashin jagorancin mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu suka soke zaben Gwamna Mutfwang, tare da umurtar Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ba dan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Goshwe shaidar lashe zaben.
Mutfwang, wanda ya bayyana hakan a cikin takaitaccen bayaninsa a Kotun Koli mai mambobi takwas na manyan lauyoyin Najeriya karkashin jagorancin Cif Kanu Agabi, ya ce “doka a bayyane take cewa, duk inda aka yi kuskure, akwai hanyar gyara.”
Gwamna Mutfwang wanda a ranar Talata ne ake sa ran za a saurari takaitaccen bayaninsa a Kotun Koli, ya buƙaci kotun da ta ayyana shi a matsayin zababben Gwamnan Filato.
Ya ce: “An hada batutuwa takwas kuma an gabatar da su a gaban kotun da ke kasa domin tantancewa, amma abin takaici, batu guda daya ne kawai (na shari’a) kotun ta daukaka, ta yanke shawarar barin batutuwa bakwai da ba a taba su ba.”
“Wannan kotu ta bayyana a lokuta da dama cewa, ya kamata kotunan tsaka-tsaki su bayyana dukkan batutuwan da aka gabatar a gabansu. Kada ta tsaida shi kan wani batu ɗaya ko ra’ayi a yi watsi da sauran batutuwa.
Mutfwang ya dage cewa tun da ba a yi masa adalci a Kotun Daukaka Kara ba, ya kamata Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin na Kotun Daukaka Kara na soke zabensa.