Kotun daukaka kara ta raba gardamar sarautar Barebarin Jihar Legas

Shekaru 14  da ’yan kabilar Barebari suka yi a Jihar Legas ba su da tsayayyen shugaba ya zama tarihi, sakamakon raba gardama da kotun daukaka kara a jihar ta yi, yayin da ta  tabbatar da Alhaji Mai Sale Mustafa a matsayin sarkin.Tun a shekarar 2001 ne Alhaji Mai Sale ya maka Alhaji Mustafa Mohammed kotu […]

Kotun daukaka kara ta raba gardamar sarautar Barebarin Jihar Legas

Shekaru 14  da ’yan kabilar Barebari suka yi a Jihar Legas ba su da tsayayyen shugaba ya zama tarihi, sakamakon raba gardama da kotun daukaka kara a jihar ta yi, yayin da ta  tabbatar da Alhaji Mai Sale Mustafa a matsayin sarkin.
Tun a shekarar 2001 ne Alhaji Mai Sale ya maka Alhaji Mustafa Mohammed kotu a kan ikirarin cewa shi ne Mai Kanuribe na Jihar Legas. An yi ta tafka shari’a, har sai a ranar 20 ga watan Maris  na shekarar 2009 Mai shari’a Olateru Olagbegi ya yanke hukuncin cewa Alhaji Mai Sale Mustafa shi ne Sarkin Barebarin Jihar Legas, biyo bayan hujjojin da shaidun da suka nuna yadda Alhaji Mustafa ya zama shugaba ya saba wa yadda ’yan kabilar ke zaben shugabansu. A kan haka ne ya yanke hukuncin cewa Alhaji Mustafa Mohammed ya daina ikirarin shi ne Mai Kanuribe na Jihar Legas.
Wannan hukuncin bai yi wa Alhaji Mustafa dadi ba, saboda haka ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2013 ya daukaka kara, inda kuma alkalan kotun daukaka karar, su 3, suka tabbatar da  shari’ar kotun farko, lamarin da ya kara tabbatar da cewa Alhaji Mai Sale shi ne Mai Kanuribe na Legas.
Dangane da abin da zai yi wajen hada  kan Barebari mazauna Legas, sai Alhaji Mai Sale Mustafa ya ce, “Da ma ba wani fada ko sabani cikinmu illa dai mu tantance wane ne shugaba, kuma ya san matsayinsa da kuma rawar da zai taka a lokacin da  bukatar hakan ta taso”.
Da wakilin Aminiya ya nemi jin ta bakin wanda aka hana ci gaba da kiran kansa a matsayin Mai Kanuribe na Legas, Alhaji Mustafa Mohammed game da wannan hukuncin, sai ya ce tunda bai ga takardar da ke dauke da hukuncin ba, ba wani abin da zai ce.