Kotun daukaka kara ta soke hukuncin soke rajistar Jam’iyyar ADC da wasu 4

A safiyar Talata Kotun Daukaka karar ta yanke sabon hukuncin tare da bayyana umarnin kotun farkon a matsayin haramtacce.

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin soke rajistar Jam’iyyar ADC da wasu 4

Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta jingine hukuncin Babban Kotun Tarayya da ya bayar da umarnin soke rajistar jam’iyyun ADC da Accord da wasu jam’iyyu uku.

A safiyar Talata Kotun Daukaka karar ta yanke sabon hukuncin tare da bayyana umarnin kotun farkon a matsayin haramtacce.

Aminiya ta ruwaito cewa Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne bayar da umarnin farko ga umarnin kotin farko ga hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyun ADC, APP, AA, Accord, AP, ZLP, bisa hujjar rashin tabukawarsu a zaben shekarar 2023.

Daga bisani jam’iyyun suka daukaka kara suna neman a soke hukuncin.

A yayin yanke hukuncin, kotun daukaka karar ta bayyana cewa umarnin kotun farko na soke rajistar jam’iyyun haramtacce ne, kuma raini ne ga umarnin Kotun Koli.

Alkalan kotun daukaka karar karkashin Mai Shari’a Abba Mohammed, sun yi ittifakin cewa tun fa farko bai kamata Babbar Kotun Tarayyar ta saurari karar ba.

Sun kara da cewa alkalin babbar kotun ya tafka kuskure ta hanyar ci gaba da sauraren shari’ar bayan umarnin kotu na dakatar da hakan, saboda wanda ya nemi hakan ba shi da hurumin yin haka.