Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti na NNPP

Kotun ta tace tun farko kotun sauraron kararrakin zaben ba ta yi daidai ba da ta baiwa Hon. Musa Ilyasu Kwankwaso na Jam’iyyar APC kujerar.

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti na NNPP

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam Yusuf Datti na Jam’iyyar NNPP.

Kotun ta tace tun farko kotun sauraron kararrakin zaben ba ta yi daidai ba da ta baiwa Hon. Musa Ilyasu Kwankwaso na Jam’iyyar APC kujerar.

Da farko Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Majalisar Jihohi da Tarayya ta soke nasarar Yusuf Datti, kan zargin kan rashin ajiye aikinsa na malumnta a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) kwana 30 kafin zaben da ya tsaya takara.

Jagorar kwamitin alkalan mai mutum uku, Mai Shari’a Flora Ngozi-Azinge, ta kuma bayyana cewa wanda ake zarign ya gaza gamsar da kotun cewa shi halastaccen dan jam’iyyar NNPP ne.

Saboda haka ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta janye shaidar cin zaben da ta ba shi, ta mika wa babban abokin hamayyarsa kuma wanda ya zo na biyu, Musa Ilyasu Kwankwaso na APC a matsayin wanda ya ci zaben.

Amma a karar da ya daukaka, kotun daukaka karar ta ce hukuncin kotun farkon ba daidai ba ne, don haka ta dawo masa da kujerar da ya ci a zaben na ranar 25 ga watan Fabarairu, 2023.