Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Gwamnan Ishaku

Kotun Daukaka Kara da Abuja ta tabbatar da zaben Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba. Kotun ta kuma yi watsi da karar da Jam’iyyar APC ta daukaka kan rashin cancanta, inda ta amince da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar cewa mai karar ba ta da dan takara a zaben Gwamna na ranar 9 […]

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Gwamnan Ishaku

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku

Kotun Daukaka Kara da Abuja ta tabbatar da zaben Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba. Kotun ta kuma yi watsi da karar da Jam’iyyar APC ta daukaka kan rashin cancanta, inda ta amince da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar cewa mai karar ba ta da dan takara a zaben Gwamna na ranar 9 ga  Maris 2019 a jihar. Kotun mai alkalai biyar ta amince da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe, wacce ta yanke hukuncin korar karar da Jam’iyyar APC ta shigar.

A hukuncin da ta yanke kotun ta yarda cewar Jam’iyyar APC da ta shigar da karar  ba ta da dan takara a zaben Gwamnan da aka gudanar a Jihar Taraba, sakamakon hana dan takararta Abubakar Danladi yin takara da Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo ta yi.