Kotun Daukaka Kara ta tabbatar wa Gwamnan Benuwe nasara
Kotun ta yi watsi da ƙarar a kan cewa lamarin ya kasance na kafin zaɓe.
Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja, a ranar Litinin ta tabbatar da zaben Hyacinth Alia, na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan Benuwe.
Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Titus Uba ya garzaya kotun daukaka kara saboda bai gamsu da hukuncin karamar kotun da ta tabbatar da zaben Alia ba.
- Saura ƙiris Matawalle ya karɓi kujerarsa a Zamfara — APC
- Sojoji Sun Kashe ’Yan ISWAP A Kwalekwale A Tafkin Chadi
A kotun, Uba ya yi zargin cewa mataimakin Alia, Samuel Ode, ya gabatar da takardar shaidar jabu ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa kuma hakan ya saba wa sashe na 182(1)(j) na Tarayyar Najeriya, 1999 (da aka yi wa gyaran fuska).
Ya kuma yi ikirarin cewa an mika sunan Alia, a ƙasa da kwana 180 kafin ranar zaben, sannan Samuel Ode ba a miƙa shi ga hukumar zaɓe ba, bayan da jam’iyyar ta sake gudanar da zaben fidda gwani.
Kotun karkashin Mai shari’a Ibrahim Karaye, ta yi watsi da ƙarar a kan cewa lamarin ya kasance na kafin zaɓe.
A watan Satumbar da ya gabata ne Kotun Sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan Jihar Benuwe da ta yi zamanta a Makurdi, ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam’iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
Tun a wancan lokaci dai kotun ta yi watsi da karar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Titus Uba, ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar sakamakon zaɓen.
Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraron batun da aka kai mata.
Tawagar alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Karaye, sun bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar ne saboda abin da aka kai mata ya shafi batutuwa ne na gabanin zaɓe kamar yadda yake a sashe na 285 na Dokar Zaɓe.
Mista Titus na zargin Mista Alia da gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta jabu a lokacin da ya tsaya takara.
Sai dai kotun ta ce a gaban Hukumar Zaɓe ta INEC ya kamata ya kai ƙorafinsa.
Sakamakon zaɓen da INEC ta fitar a wancan lokaci, ya nuna cewa Mista Alia ya samu nasara ne da kuri’u 473,933, inda ya doke takwaransa na PDP, Titus Uba, wanda ya samu kuri’u 223,913.