Kotun Duniya ta bai wa Isra’ila umarnin dakatar da kai hare-hare Gaza

Hare-hare a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,857 — galibinsu jarirai da mata da yara.

Kotun Duniya ta bai wa Isra’ila umarnin dakatar da kai hare-hare Gaza

Kotun Duniya ICJ ta bai wa Isra’ila umarnin gaggauta dakatar da hare-haren sojin da take yi a Rafah da ke Kudancin Gaza.

Shugaban Kotun Nawaf Salam ne ya gabatar da umarnin wanda ya ce matakin ya zama wajibi lura da irin halin da ake ciki.

Ya ce saboda haka kotun tana mai ba da umarnin gaggauta dakatar da hare-haren da Isra’ilar ke kai wa a Rafah kamar yadda kasar Afirka ta Kudu ta bukata a ƙarar da ta shigar.

Yayin da ake gabatar da hukuncin, wasu masu goyan Falasɗinawa a wajen kotun sun yi ta daga tuta suna bayyana bukatar ’yantar da Falasɗinu.

Isra’ila ta daɗe tana watsi da zargin da ake mata na aikata laifuffukan kisan kiyashi yaki, inda take cewa matakin sojan da take ɗauka tana yinsa ne domin kare kanta sakamakon harin da mayaƙan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktobar da ta gabata.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Isra’ila ya shaida wa duniya jiya Alhamis cewar babu wani mahaluki a duniya da zai hana Israial kare kan ta da kuma kai hari a kan maya5kan Hamas dake Gaza.

Kotun ICJ ba ta da ikon tursasawa amma duk wani hukunci da ta yanke bai yi wa Isra’ila daɗi ba yana da tasiri a idon duniya.

A wannan watan ne Isra’ilar ta ƙaddamar da hare-hare a Rafah, abin da ya tilasta wa dubban Falasɗinawa tserewa daga birnin wanda ke ƙunshe da ’yan gudun hijira sama da miliyan 2 da dubu 300.

Tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura, duk da matsin lamba da ake yi a gida ga Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na ganin an sako mutanen da a ka yi garkuwa da su a Gaza.

Isra’ila ta kwashe kwana 231 tana kai hare-hare a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,857 — galibinsu jarirai da mata da yara.

An jikkata sama da mutum 80,293, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Falasɗinu WAFA ya ruwaito.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou