Kotun ICC ta ce ta karbi koke kan Patience Jonathan

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato (ICC) ta sanar da karbar korafin Jam’iyyar adawa ta APC ta Najeriya, kan kalaman uwargidan shugaban kasar Patience Jonathan ta yi, na kira a jefi duk wanda ya ambaci kalmar chanji. Babbar mai gabatar da kara a kotun da ke birnin Hague, Fatou Bensouda ta ce suna nazari […]

Kotun ICC ta ce ta karbi koke kan Patience Jonathan
Kotun ICC ta ce ta karbi koke kan Patience Jonathan

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato (ICC) ta sanar da karbar korafin Jam’iyyar adawa ta APC ta Najeriya, kan kalaman uwargidan shugaban kasar Patience Jonathan ta yi, na kira a jefi duk wanda ya ambaci kalmar chanji.

Babbar mai gabatar da kara a kotun da ke birnin Hague, Fatou Bensouda ta ce suna nazari kan korafin kuma za su “gudanar da binciken da ya dace.”
Mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar APC, Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC cewa kotun ta samun wasikar korafin da suka gabatar mata. Har ila yau, a wata sanarwa da kotun ta aike wa jaridar Punch a ranar Litinin ta ce uwargidan shugaban kasar za ta iya fuskantar tuhuma daga kotun, inda ta ce har ta fara bincike kan batun.
A farkon wannan watan ne mai dakin shugaban kasar Patience Jonathan lokacin gudanar da yakin neman zabe a garin Kalaba na Jihar Kurus Ribas, inda aka ruwaito ta tana kira ga magoya bayan jam’iyyarsu da su jefi duk wanda ya fada masu taken canji, wanda shi ne lakabin jam’iyyar adawa ta APC ne.
Wannan na zuwa ne watanni bayan da manyan ‘yan takarar shugabancin kasar biyu: Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da Shugaba mai ci Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP, suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.