Kotun Kano ta umarci magidanci ya yanka zakaransa
Makwabcin mai zakaran ne ya kai kara saboda yana samunsa da cara
Wata kotun majistare da ke Gidan Murtala a Jihar Kano ta umarci wani mutum, Isyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin na Kano da ya yanka zakaransa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Halima Wali, ce ta yanke hukunci yayin zaman kotun na ranar Talata.
- NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 144 da suka makale a Nijar
- Matar Gwamnan Kano na farko, Audu Bako, ta rasu
Tun da farko Makwabcin Isyaku mai suna Malam Yusuf Muhammad Ja’en ne ya shigar da karar a gaban kotun cewa zakaran yana shiga hakkinsa, inda yake hana shi barci da yawan cara.
Lokacin da aka karantowa wanda ake kara takardar karar, ya ce gaskiya ne zakaran na yawan yin cara kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” don haka ya roki kotun da ta sahale masa zuwa ranar.
Alkalin kotun ta amince da rokon nasa inda ta umarce shi da ya killace zakaran .
Sannan ta kuma umarce shi da ya yanka shi a ranar Jumu’a mai zuwa wato ranar “Good Friday” din.