Kotun Koli da batun kujerar Gwamnan Bayelsa
A wani mataki da suka dauka, alkalai biyar na Kotun Koli sun yi wa siyasar Bayelsa juyin waina bayan da suka soke nasarar da Cif David Lyon na Jam’iyyar APC ya yi a zaben Gwamna, kasa da awa 24 kafin a rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar. Kotun ta bayyana cewa tunda dai Cif […]
A wani mataki da suka dauka, alkalai biyar na Kotun Koli sun yi wa siyasar Bayelsa juyin waina bayan da suka soke nasarar da Cif David Lyon na Jam’iyyar APC ya yi a zaben Gwamna, kasa da awa 24 kafin a rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar.
Kotun ta bayyana cewa tunda dai Cif Biobarakuma Degi-Eremieoyo yana takara ce tare da Cif Lyon, to kuwa tabbatar da rashin cancantarsa ta shafi zabensu a matsayin ’yan takarar APC.
Tunda farko wata kotu ta yanke hukuncin cewa Mataimakin Lyon, Degi-Eremieoyo ya bada takardun bogi wanda haka ya sanya bai halatta ya tsaya a zaben Gwamnan da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba bara ba tunda farko. Wannan hukunci dai ya zo ne bayan Jam’iyyar PDP ta shigar da kara a Kotun Daukaka inda dan takararta Cif Douye Diri da Mataimakinsa Cif Lawrence Ewhrudjakpo suka kalubalanci nasarar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ita kuma saboda bin hukuncin da kotu ta yanke, a ranar Juma’ar da ta wuce sai ta mika wa dan takarar PDP Cif Diri da Mataimakinsa takardar shaidar cinye zabe, kuma nan da nan aka rantsar da shi, rantsuwar da ya sha a wurin ajiye motocin gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa, wanda yake kewaye da matakan tsaro.
Wannan hukunci na Kotun Koli, ya girgiza Cif Lyon da Jam’iyyar APC, ganin yadda tuni ya gama shirye-shiryen kama madafun ikon jihar. A ran Alhamis wacce ta kasance jajibirin wannan hukunci, ya je filin wasa na Samson Siasia inda ya koyi yadda ake hidimomin karbar mulki ciki har da yadda ake duba faretin soja da za su gudanar a wajen bikin rantsar da shi.
Ko da a ranar Laraba, sai da aka maye tutocin PDP da ke gaban gidan gwamnati da tutar APC a garin Yenagoa, a daya daga cikin shirye-shiryen bikin karbar mulkin da ake yi. Sannan kuma akwai wata lacca da ka shirya yi a ranar Asabar wacce kuma ake sa ran Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ne zai jagorance ta tare da sa ran manyan baki da dama musamman daga Jam’iyyar APC za su je wurin.
Wannan hukunci da kotun ta zartar ya sanyaya jikin jama’a da dama a jihar musamman ma kusoshi Jam’ iyyar APC, inda har ta kai ga Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Adams Oshiomhole ya kasa kintse fushinsa inda ya fito fili ya ce a ranar Juma’a babu wani mutum da za a rantsar a matsayi Gwamnan Bayelsa in ba Cif Lyon wanda shi ne dan takarar APC ba.
Wannan har ya kai ga tashin-tashina, inda wadansu samari suka dauki doka a hannunsu suka fantsama suna zanga-zangar da ta juye zuwa lalata muhimman wurare da suka hada da gidan tsohon Gwamnan Bayelsa Sarieke Dickson da Dakin Karatu na Stebe Azaiki da Gidan Rediyon Bayelsa da wani gida na Mista Diri da kuma wani bangare na ginin Sakatariyar PDP.
Wannan yanzu ya nuna cewa ’yan takarar APC da kuma Shugaban APC Oshiomhole suna fuskantar wani yanayi na kalubale. Musamman ganin cewa a karshashin jagorancinsa an yi ta samu kura-kurai masu sosai rai wadanda kuma suka sanya jam’iyyar ta rasa wasu manyar kujerunta a kotuna.
Hakan ya farp ne daga Jihar Ribas inda rashin fahimtar juna a tsakanin wadansu ’ya’yan jam’iyyar ya yi sanadiyyar kotu ta haramta wa jam’iyyar tsaida dan takara a zaben Gwamna da na ’yan majalisa. Sai kuma badakalar Zamfara da kuma wannan cakwakiya ta Bayelsa.
Dole jam’iyyar ta yarda cewa ta samu tangardar cikin-gida game da yadda take fitar da ’yan takara. Sannan tilas shi ma shugabanta ya daina kokarin yi wa hukuncin kotu karan-tsaye.
Haka kuma wannan abin da ya faru wata manuniya ce ga sauran ’yan siyasa cewa cin wani mukami ba wai magana ce ta ko a mutu ko a yi rai ba ko kuma in ba ni ba kowa ya rasa.
Haka kuma wannan hukunci da kotun ta zartar ranar Alhamis yana nuna amfanin jajircewa a kan bin hakki a gaban kotu duk kuwa da yake hakan yana da wahala matuka. Jam’iyyar PDP ma tana ta raki a kan hukuncin da kotu ta yanke game da karar Jihar Imo, inda ta kai har tana caccakar fannin shari’a, wanda kuma duk irin yadda ba ta ji dadin hukuncin ba, wannan irin caccaka ba za ta taba haifar da da mai ido ba.