Kotun Koli: Muna son a yi adalci a shari’ar zaben Kano —’Yan Kannywood
Wasu jaruman Kannywood sun roki Shugaba Tinubu da ya tabbatar da an yi adalci a shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano da ke tafe a kotun koli.
Jaruman Kannywood sun roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar Kotun Koli ta yi adalci a hukuncin da za ta yanke a shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano da ke gabanta.
Fitaccen jarumin Kannywood, Sani Danja ne ya yi wannan roko a taron manema labarai da wasu jaruman Kannywood suka yi a Kano ranar Asabar.
- Sojoji sun kashe dan ta’adda Ali Kachalla da kwamandojin Dogo Gide
- Gwamnatin Borno na raba wa ’yan gudun hijira dabbobi 5,000
Sani Danja ya ce matsayin ’yan Kannywood na ’yan Najeriya masu kishin, suna kira ga Tinubu da ya gaggauta tabbatar da adalci da gaskiya a shari’ar zaben gwamnan Kano a Kotun Koli, wanda ake sa ran yanke hukunci nan gaba.
“Masu kishin kasa da dama da ma shugabannin da suka shude sun yi tsokaci a lokuta daban-daban kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan Kano.
“Don haka muna fatan shugaban kasarmu, a matsayinsa na uba, zai yi la’akari da hakkin ’yan Kano da kuma tabbatar da adalci,” in ji shi.
Sani Danja ya bayyana cewa Jihar Kano ta kasance cikin zaman lafiya amma hukuncin kotun daukaka kara, na neman mayar da hannun agogo baya.
“Muna rokon shugaba Tinubu da duk masu ruwa da tsaki kada su bari ra’ayi da bangaranci su bata harkar shari’ar kasar nan,” in ji kakakin na ’yan Kannywood.