Kotun Koli ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira

Kotun Kolin Najeriya ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira har sai sabin da hali ya yi.

Kotun Koli ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira

Naira

Kotun Kolin Najeriya ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira har sai sabin da hali ya yi.

A zaman Kotun Kolin na ranar Laraba, Mai Shari’a John Okoro wanda ya jagoranci sauran alkalai shida, ya ce babu ranar daina amfani da tsofaffin takardun kudaden da CBN ya sauya wa fasali.

Ya kara da cewa za tsofaffin kudaden za su ci gaba aiki kafada-da-kafada da sabbabbin da aka yi, har sai lokacin da bankin CBN ya gama maye gurbin tsofaffin da sababbi da kuma cika ka’idojin da suka kamata.

Mai Shari’a John Okoro ya ce, “tsofaffin N200, N500, da N1000 naira za su rika aiki tare da sabbin da aka yi har zuwa lokacin har zuwa lokacin da gwamnati ta yanke shawarar daina amfani da tsofaffin bayan ta tuntubi masu ruwa da tsaki da kuma tanadar duk abubuwa da suka kamata.”

Kotun Kolin ta yanke hukuncin ne baya karar da Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Kasa, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar na neman kotun ta soke wa’adin ranar 31 ga watan Disamba 2023 na daina amfani da tsoffin takarduna N200 da N500 da kuma N1,000.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ne ya kawo batun sauyin takardun kudin da kuma takaita cirar tsabar kudi, gabanin zaben 2023, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

Duk da umarnin kotu na hana sauyin kudin, CBN na shirin dakatar da amfaninsu a ranar 31 ga watan Disamba, daga bisani ta ce za a ci gaba da amfani da su, zuwa lokacin da za ta kammala tuntubar masu ruwa da tsaki kan matakin da kuma shirinta na zuwa kotu domin samun izinin soke wa’adin na 31 ga wata Disamba.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024