Kotun koli ta cire sarki a Filato bayan shekara 31 a kan kujera

Kotun koli da ke Abuja ta soke nadin wani basarake a Jihar Filato mai suna Nde Goyang Kayili na Somji da ke gundumar Kabwir a karamar Hukumar Pankshin shekara 31 bayan shigar da kara a kansa. Mai shari’a Clara Ogunbiyi, ta fadi a cikin hukuncin da ta yanke ranar Juma’ar da ta gabata cewa, daukaka […]

Kotun koli ta cire sarki a Filato bayan shekara 31 a kan kujera
Kotun koli ta cire sarki a Filato bayan shekara 31 a kan kujera

Kotun koli da ke Abuja ta soke nadin wani basarake a Jihar Filato mai suna Nde Goyang Kayili na Somji da ke gundumar Kabwir a karamar Hukumar Pankshin shekara 31 bayan shigar da kara a kansa.

Mai shari’a Clara Ogunbiyi, ta fadi a cikin hukuncin da ta yanke ranar Juma’ar da ta gabata cewa, daukaka karar da lauyan Kayili ya yi kan hukuncin Kotun daukaka kara ta Jos ba ta da madogara don haka ta yi watsi da ita. Sauran alkalan kotun su ne Mai shari’a Ibrahim Tanko da John Fabiyi da Dattijo Mohammed da kuma Kudirat Kekere-Ekun.
A hukuncin da suka cimma matsaya kotun ta ce uwar karar da aka daukaka da kuma daukaka kara a kan daukaka kara ba su da tushe kuma sun yi watsi da su, sai dai ba su ce a biya kowa ko kwabo ba a tsakanin abokan shari’ar.
Kotun ta ce Kotun daukaka kara ta yi daidai da ta ce sarautar Somji za a rika karba-karba ne a tsakanin gidajen sarauta biyu na Neha da Ne’es. Ta kuma amince da hukuncin Kotun daukaka karar cewa gidan sarauta na Neha kadai ne yake da ’yancin hawa kujerar sarautar bayan mutuwar Nde Boyi Goshit daga gidan sarauta na zuriyar Ne’es a ranar 5 ga Satumban 1984.
Mai kara, Esly Yilbuk da wasu mutum biyu wadanda suka mutu sun shigar da karar ce a 1987, suna kalubalantar nada Kayili a maimakon gidan sarauta na Neha.