Kotun Koli ta dage sauraron shari’ar Canjin Kudi
Kotun Koli ta sanya 3 ga watan Maris, 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari’ar
Kotun Koli ta sanya 3 ga watan Maris, 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari’ar da ke kalubalantar dokar sauyin kudi da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Alkalan Kotun su bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro sun sanar da haka ne a zaman kotun na ranar Laraba.
- Zulum ya ba wa ‘yan sanda kyautar motocin sulke 9
- Kai Tsaye: Shari’ar Sauyin Kudi daga Kotun Kolin Najeriya
Daga nan suka dage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Maris mai kamawa.