Kotun koli ta dakatar da shari’ar Saraki

Kotun koli ta bayar da umurnin dakatar da shari’ar Shugaban Majalisar Dattiojai, Bukola Saraki, da ke gaban kotun da’ar ma’aikata.Mista Saraki na fuskantar tuhumar laifuka 13 na cin hanci a wannan kotun. Ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da su, na kin bayyana hakikanin dukiyarsa.Manyan alkalan Babbar Kotu da ta daukaka kara sun ki […]

Kotun koli ta dakatar da shari’ar Saraki
Kotun koli ta dakatar da shari’ar Saraki

Kotun koli ta bayar da umurnin dakatar da shari’ar Shugaban Majalisar Dattiojai, Bukola Saraki, da ke gaban kotun da’ar ma’aikata.
Mista Saraki na fuskantar tuhumar laifuka 13 na cin hanci a wannan kotun. Ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da su, na kin bayyana hakikanin dukiyarsa.
Manyan alkalan Babbar Kotu da ta daukaka kara sun ki amincewa su yi watsi da karar.
Kafin zartar da hukuncin, sai da Kotun daukaka kara ta dan dakatar da shari’ar na wani dan lokaci.
A jiya Alhamis, sai Kotun koli ta ce karar cin hanci da ake tuhumar Saraki da ita, “a dakatar da ita” har sai an kammala sauraren karar da aka daukaka a gabanta.
Kotun kolin ta bayyana aniyarta na bin kadin al’amarin ba tare wani bata lokaci ba.