Kotun Koli ta kori dan takarar gwamnan APC na Taraba

Kotun Koli ta soke Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar APC

Kotun Koli ta kori dan takarar gwamnan APC na Taraba

Kotun kolin Najeriya

Kotun Koli ta soke Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar APC.

A ranar Laraba lauyoyi biyar na Kotun Kolin, karkashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun suke soke dan takarar.

Gabanin haka, sai da Babbar Kotun Tarayya ta kori Sanata Bwacha bayan karar da David Sabo Kente, wanda ya nemi tsayawa takarar gwamna a Jam’iyyar APC ya sigar a watan Satumban 2022.

Kotun Kolin ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayyar bisa hujjar cewa haramtacce ne zaben dan takarar Gwamnan Taraba da APC ba ta gudanar, wanda ya samar da Bwacha.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno