Kotun Koli ta rantsar sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya 72
Babban Alkalin Najeriya bai halarci taron rantsar Manyan Lauyoyin ba
Kotun Koli ta Najeriya ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) guda 72 a safiyar Litinin.
Sai dai Shugaban Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Tanko, wanda shi ya kamata ya jagoranci taron bai halarta ba.
- ’Yan daba sun tsarwatsa taron samar da tsaro a Arewa
- Sojoji sun zagaye dajin da aka kai daliban da aka sace
- Dalibai 333 ne suka bace a GSSS Kankara —Masari
- Amurka ta tabbatar da yi mata kutse a shafukan intanet
Sakamakon haka alkali mafi girma a Kotun Koli, Mai Shari’aOlabode Bodes-Rhodes Vivour ce ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin a madadinsa.
An ba wa lauyoyin matsayin na SAN ne a matsayin shaidar gwanancewa a manazarta kuma masu kare hakki.
A watan Nuwamba ne Kwamitin Alfarmar Ayyukan Shari’a ya amince da daga martabar lauyoyi 72 zuwa matsayin SAN.
Da take ba su rantsuwa, Mai Shari’a Rhosdes-Vivour ta yi jan kunne ga masu saba wa umarnin kotu.
Bisa al’adar taron an shekara-shekara, Shugaban Alkalan Najeriya ne ke jagorantarsa; ba a samu bayanin dalilin rashin halartar Mai Shari’a Muhammad Tanko taron na 2020 ba.