Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule a Nasarawa

Kotun ta ce tun da farko dan takarar PDP bai shigar da karar bisa ka’ida ba.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule a Nasarawa

Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, David Umbugadu, ya shigar kan zaben Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa.

Kotun ta kori karar kan rashin cancanta, amma ba ta ci tarar dan takarar na jam’iyyar PDP ba.

A ranar 2 ga watan Oktoba, 2023 kotun sauraron kararrakin zabe da ke Lafiya, ta soke nasarar Gwamna Sule tare da ayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hakan ne ya sanya, Gwamna Sule da jam’iyyar APC suka daukaka kara tare da neman kotun daukaka kara ta soke hukuncin da kotun kasa ta yi.

Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke na ranar 23 ga watan Nuwamba, 2023 ta soke hukuncin kotun kasa, tare da tabbatar da zaben Sule a matsayin gwamnan Nasarawa.

Kotun daukaka kara, ta ce kotun kasa ta yi kuskure wajen ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai PDP da dan takararta ba su gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, hakan ne ya sanya suka garzaya kotun koli, domin neman soke nasarar Abdullahi Sule.