Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Dare na Zamfara

Kotun Kolin ta yi watsi da hukuncin da ke cewa Zaben Gwamnan Zamfara wanda bai kammala ba.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Dare na Zamfara

Alhaji Dauda Lawal Dare

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Zamfara.

Kotun Kolin ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wadda ta bayyana zaben gwamnan a matsayin wanda bai kammala ba, kuma ta bayar da umarnin sake zabe a wasu kananan hukumomi uku na jihar.

Hukumar zaɓe dai ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.

Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi INEC da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume