Kotun Koli ta tabbatar da tuhumar ta’addanci kan Nnamdi Kanu
Kotun koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara na sakin Nnamdi Kanu da ake zargi da cin amanar kasa da Gwamnatin tarayya take yi masa
Kotun koli ta tabbatar da tuhumar ta’addanci da cin amanar kasa da ake yi wa Shugaban Kungiyar IPOB da ke neman ballewa da Najeriya, Nnamdi Kanu.
Kotun koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta ba da umarnin sakin Nnamdi Kanu wanda Gwamnatin tarayya take zargi da cin amanar kasa da kuma ta’addanci.
Kotun kolin ta ce duk da cewa an dawo Nnamdi Kanu Najeriya ba bisa ka’ida ba daga kasar Kenya, a lokacin da ya tsallake beli, amma hakan ba zai iya hana kotun shari’ar ta ci gaba da shari’a ba.
A shekarar 2015 ne aka fara tsare Nnamdi Kanu, inda bayan kotu ta ba da belinsa ya tsere daga Najeriya zuwa kasar Birtaniya bayan wani hari da sojoji suka kai gidansa.
- Kotun Koli: Uban jam’iyyar NNPP ya shirya addu’ar roka wa Abba nasara
- Yadda tsadar magunguna ke jefa marasa lafiya cikin kunci
A kan haka ne kotun ta soke belin ta kuma bukaci a kamo maya shi, inda daga bisani hukumar tsaro ta DSS ta tiso keyarsa daga kasar Kenya domin ci gaba da gurfanar da shi.
Sai dai ya daukaa kara da cewa kotun ba ta da hurumin ci gaba da gurfanar da shi saboda ba a bi ka’ida ba wajen dawo da shi Najeriya.
Bisa haka ne kotun daukaka karar ta umarci gwamnati ta sake shi, hukuncin da gwamnatin ta daukaka kara a kai.
A hukuncin kotun Koli na ranar Juma’a, alkalanta biyar sun yi ittakin cewa kotun daukaka kara tana da hurumin gurfanar da shi.
Ta bayyana cewa saba ka’ida wajen dawo da shi Najeriya daga kasar wajen ba zai soke tuhumar da ake masa ba.
A hukuncin alkalan, wanda Mai Shari’a Emmanuel Agim, ya karanta, sun soki gwamnati kan yadda ta taso kearsa daga Kenya da baruniyar hanya.
Haka kuma ta soki kotun farko da ta soke belin Nnamdi Kanu, saboda tserewar da ya yi don tsira da rayuwarsa a lokacin da sojoji suka kai hari gidansa.
Tun shekarar 2021 da DSS ta dawo da shi daga kasar Kenya yana tsare.